Shugaban APC na karamar hukumar Gezawa ya sauke wa daliban da su ka sauke al’qur’ani kabakin arziki

Date:

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo

 

Alhaji Sani yanmedi Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Gezawa, ya ba da tallafin atamfofi ga da daliban da suka sauke al’qur’ani mai girma a makarantar Tarbiyyatul Aulad dake jannarya a karamar hukumar Gezawa.

Alhaji Sani yanmedi ya ce ya ba da kyautar Atamfofin tare da kudin dinki naira Dubu Dari domin kara zaburar da daliban wajen cigaba da kokarin zuwa makaranta domin samun ilimin Addini, ya ce kuma hakan zai sa sauran dalibai na baya su kara zage dantse wajen cigaba da zuwa makaranta.

Talla

Ya kara da cewa “Hakika irin wadannan Dalibai ya dace a rika kokarin taimaka musu duba da yadda suka maida hankali wajen zuwa makaranta har Allah ya ba su damar sauke Al’qur’ani mai girma, dan haka babu tukuicin da ya kamata a yi wa daliban sai da irin wanan tagomashi kuma ashirye muke mu cigaba da tallafawa makaratun islamiyyu da dalibai a Gezawa baki daya.

Sanya Al’adu A Fina-Finai Na Iya Inganta Harkar A Nahiyar Afirika – KILAF

Kazalika Shugaban jam’iyyar ya yi kira ga matasa da su maida hankali wajen neman ilimin Addini domin shi ne zai taimake su a duniya da lahira.

Daga karshe ya yi wa wadannan dalibai fatan Alkairi tare da Fatan za su yi amfani da abin da suka karanta domin samarwa da kansu gobe mai kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...