Daga Sani Idris Maiwaya
Jarogan taron kasa da kasa da KILAF ta shirya a Kano Malam Abdulkarim Muhammad ya ce sanya al’adu a fina-finan Nahiyar Africa zai taimaka matuka wajen inganta Sana’ar a Nahiyar baki daya.
Malam Abdulkarim Muhammad ya bayyana hakan ne yayin taron ba da kyaututtuka ga yan masana’antar Shirayar Fina Finai a ciki da wajen Nigeria .
Ya ce akwai bukatar baiwa al’adu mahimmaci a cikin Fina finai dan ciyar da harkar gaba kamar yadda ake yi a sauran nahiyoyin duniya.

Malam Abdulkarim yace hakan ce tasa kungiyar KILAF ta ware lokaci dan ba da kyautuka ga masu Shirya fina-finai da masu bada umarni sai Jarumai mata da maza ba kuma masu tace hoto
Abdulkarim yace wannan shi ne karo na bakwai da kungiyar KILAF take shirya irin wannan taro .
Mahalarta Taron KILAF 24 Sun Yaba da Yadda Kano ta Adana Kayan Tarihinta
Shi ma a nasa jawabin Gwamnan kano injiniya Abba kabir Yusuf ya yaba da yadda a jihar kano ta karbi bakuncin taron da wakilai suka halarta daga ciki da waken kasar Nigeria.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar ma’aikatar yawon bude ido Hajiya Ladidi Garko, yaa taya wadanda suka sami kyautukan murna, Sannan kuma ta bukace su suka jajircewa wajen ba da gudummawa musamman a fannin Al’adu a cikin Fina-finan na su .
Jarumi Yakubu Muhammad shi ne wanda ya zamo gwazon jarimi sai Fim Din KAKA da aka bashi lambar yabo ta ingacin labari, yayin da fim din GIDAN DAMBE ya kasancce zakaran gwajin dafi da yayi fice a cikin Fina-finai da suka shiga gasar
Shi ma a nasa bangaren Shugaban Hukumar tace Fina finai ta jihar kano Abba Almustapha ya Shaidawa wakilin KADAURA24 cewar tabbas an shirya taron a lokacin daya dace .
Taron dai ya samu halatar Al’umma da dama kamar su Ali Nuhu da Shugaban gidan Radion Muhasa Muhammad baban Dede da kuma wasu da dama.