Daga Umar Usman Sani mainagge
Kungiyar kare hakkin Dan Adam da tallafawa al’umma wato Awareness for human right and charity foundation wato (AWRCF) a turance ta gudanar da gangamin bayar da kyautar jini ga masu fama da lalurar Sikila a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake birnin Kano.
Da yake bayyana masudin gangamin a wannan rana shugaban kungiyar na kasa, Kwamaret Auwalu Usman Awareness ya ce sun shirya gangamin ne sakamakon korafin ƙarancin jini da Mata masu haihuwa da masu lalurar Sikila suke fuskanta a asibitin.
” Dama mun jima muna irin wannan aikin hakan ta sa muka tara mutane yan kungiyar mu da ma wadanda ba yan kungiyar mu ba, domin mu taimakawa bayin Allah da suke shiga cikin mawuyacin hali saboda ƙaranci jinin siyarwa da kuma waɗanda ma ba su da halin siya”. Kwamaret Auwalu Awareness

Ya ce tallafin jinin da suka bayar har kimanin leda dari da hamsin 150 ya kebanta ne kawai ga masu ciwon sikla da yara da kuma mata masu juna biyu.
Al’umma da dama ne dai suka halarci taron gangamin bayar da jini kyautar wadanda suka hadar da yan Kungiyar da wadanda ba ‘yan Kungiyar ba, duk domin tallafawa masu karamin karfi dake cikin al’umma.
Shugaban APC na karamar hukumar Gezawa ya sauke wa daliban da su ka sauke alqur’ani kabakin arziki
Commarade Auwal Usman ya shaidawa Kadaura24 cewa aiyukan kungiyar ta sun sun hadar da aiyukan jin kai da wayar da kan al’umma da kuma kare hakkin bil’adam.
Wasu daga cikin wadanda suka ba da tallafin jinin sun bayyana cewa sun bayar da jini kyauta ne domi domin marasa karfi cikin majinyata su amfana soboda Allah.