Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya dage dakatarwar da aka yi wa Kwamishinan ayyuka na Musamman, Auwalu Dalladi Sankara, daga yanzu nan take.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanyawa hannu.

“Za a iya tunawa cewa an dakatar da kwamishinan bisa zargin da ake yi masa kan faruwar wani al’amari daga rahotan hukumar Hisbah ta jihar Kano”, inji Sakataren Gwamnatin.
Sanarwar ta ce an dage dakatarwar ne bayan kotu ta wanke Kwamishinan.
Idan za’a iya tunawa an dakatar da Kwamishinan ne sakamakon zarginsa da mu’amala da matar aure, lamarin da ya kai ga kaisu Kotu.