Daga Isa Ahmad Getso
Cece-kuce ta barke bayan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ambaci sunan mai martaba, Muhammadu Sanusi II, a matsayin sarkin Kano na 16.
Daily Trust ta rawaito cewa Shettima ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, na ‘X’, lamarin da ya sa wasu su ka bayyana cewa ya yi biyayya tare da amincewa da sarki Sanusi a matsayin halastaccen sarkin Kano.
Duk da har yanzu ana cigaba dambarwar kujerar sarkin Kano a gaban kotu, bangaren mai martaba Aminu Ado Bayero na cigaba da ikirarin zama halastaccen sarki duk da gwamnatin jihar Kano ta sauke shi tare da nada Muhammadu Sanusi II.

A rubutun da ya fara wallafawa da farko, Shettima ya rubuta cewa; “a ranar Asabar, na halarci daurin auren diyar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.
Kwankwaso ya bayar da auren ‘yar sa, Dakta Aishatu Kwankwaso ga Fahad, da wurin hamshakin dan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.
” An gudanar da taron daurin auren ne fadar Sarkin Kano na 16 Alhaji Muhammad Sanusi II.
Rikicin Sarautar Kano: Ana neman yi mana mulkin-mallaka da katsalandan – Kwankwaso
Ina taya ango da amarya murna tare da yi musu fatan samun farinciki mai dorewa a rayuwarsu ta aure.”
Sai dai, bayan martanin wasu mutane ma’abota amfani da manhajar ‘X’, sun gyara sakon ta hanyar goge sunan sarkin Sanusi II da kuma Sarki na nawa ne ke kan mulki a yanzu.
Amma duk da haka mutane sun yi ta mayar da maryani tare da tofa albarkacin bakinsu, wasu suna ta yabawa mataimakin shugaban kasa wasu kuma suna ganin baikensa bisa ambata Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16.
Masu yabawa kashim Shettima suna cewa ya amince da Sanusi II tun da har ya kirawo shi da Sarkin Kano .
Wasu kuma suna ganin ai tunda har bai tsaya a Sarkin kano ka dai ba, sai da ya sa masa na 16 ya nuna cewa bai aminta da shi a matsayin Sarkin Kano ba.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ana cigaba da dambarwar masarautar Kano tun lokacin da gwamnatin jihar kano ta tsige Alhaji Aminu Ado Bayero tare da dawo da Sanusi II a matsayin Sarkin kano.
Sai dai na ganin sarki Aminu Ado Bayero yana da goyon bayan gwamnatin tarayya yayin da shi kuma Sarki Sanusi Ake ganin yana da goyon bayan gwamnatin jihar kano.
Har yanzu dai ana cigaba da fafata Shari’a akan batun masarautar Kanon.