Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Guda cikin jam’iyyun adawa a Kano Jam’iyyar YPP ta yabawa Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa yadda ya dauki matakan gaggawa domin magance matsalolin da suke damun al’ummar garin Danshayi dake karamar hukumar Rimin Gado, da na garin gishiri wuta dake karamar hukumar warawa.
“Matakan gaggawa da Gwamnan ya dauka akan matsalolin rashin makarantu da Ababen more rayuwa a wadancan garuru sun murgeni, kuma ni dai tun da aka dawo dimokaradiyya a Nigeria ban ga gwamnan da ya dauki irin wannan matakin cikin gaggawa ba kamar gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf “.
Shugaban jam’iyyar YPP na jihar Kano Barr. S S Umar ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya kirawo a Kano.

Idan za a iya tunawa a makon nan ne wata kafar yada labarai a Kano ta yi rahoto akan wannan gari, Inda aka rawaito cewa duk da dadewar garin da kafuwa tsahon Shekaru Dari uku Amma mutane bakwai ne kawai suka iya zuwa matakin Karatu na NCE a garin.
Rahoton ya ce dama mata a garinma ba su zuwa makarantar saboda babu makarantar a cikin gari har sai anyi tafiya kusan kilomita 15 Sannan a sami makarantar, Wanda hakan ba karamar barazana ba ce ga al’umma baki daya.
An Kuma: Wani Dan majalisar dokokin Kano ya fice daga Kwankwasiyya
” A labarin da muka samu kwamishina da mataimakin shugaban karamar hukumar sun je garin na Danshayi domin aiwatar da umarnin gwamnan, tabbas gwamnan Kano ya chanchanci yabo”. A cewar shugaban jam’iyyar YPP na Kano
Shugaban jam’iyyar ta YPP ya ce ranar da aka yi wancan rahoto washe gari gwamnan jihar kano ya tura tawaga garin domin duba matsalolinsu tare da bayar da umarnin magance matsalolin ba tare da bata lokaci ba.
” Tabbas irin wannan mataki da Gwamnan ya dauka ya yi dai-dai da manyan manufofin jam’iyyarmu ta YPP, Sannan muna yabawa gwamnan bisa yadda ya ware kaso 31 cikin dari na kasafin kudin shekara mai kamawa ta 2025″. Barr. SS Umar
Barr. S S Umar ya kuma bukaci sauran gwamnanoni da shugabanni da su yi koyi da irin wannan mataki da Gwamnan Kano ya dauka na warware matsalolin al’ummarsa cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.