Gidauniyar Najashi ta Tallafawa Mata Sama da 100 da Jari da kuma Takardun Daukar Aiki

Date:

Da Safiyar ranar Litinin Engr.Alh. Najashi Uba Ismail Gaya, wato MD UIG Oil and Gas ya kaddamar da shirin tallafawa mata Iyayen marayu da jari da kuma mika takardar daukar aiki ga Wasu matan masu kula da asibiti.

Da yake jawabi ga matan bayan raba musu jarin, Alh. Najashi ya ce ya basu jari ne domin su kula da kasu da kuma marayun dake hannun su. Ya kara da cewa wannan shirin kadan ne daga cikin irin aiyuka da wannan Gidauniya zata dinga gabatarwa lokaci bayan lokaci.

Alh. Najashi ya kuma bukaci mutanen da su ka amfana da tallafin da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace Sannan su rika sanya shi acikin addu’o’insu.

Talla

A nasa jawabin Wakiin Sarkin Gaya, ya bukaci sauran mawadata a yankin da su yi koyo da wannan abun alkhairin da Alhaji Najashi ya yi, don rage yawan mabarata da samar da aiyukan yi don bunkasa tattalin arzikin yankin.

Shi wa wakilin Gwamnan kano a wajen taron cewa ya yi, wannan Shiri ya yi dai dai-dai da manufofin Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Alh. Abba Kabir Yusuf, Kuma in Sha Allah zamu hada hannu da wannan Gidauniyar domin mu kawowa Masarautar Gaya Dama jihar Kano ci gaba.

An Kuma: Wani Dan majalisar dokokin Kano ya fice daga Kwankwasiyya

A kokarinsa na ganin ya tallafawa al’umma ko a kwanakin baya ma sai da Alhaji Najashi ya kai dauki ga sashen kula da hakori na Asibitin Sir. Sanusi da Kuma gyaran kwatoci a cikin garin gaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...