An Kuma: Wani Dan majalisar dokokin Kano ya fice daga Kwankwasiyya

Date:

Dan majalisar dokokin jihar kano mai wakilar karamar hukumar Sumaila Hon. Zubairu Hamza Massu ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya Mai littafi da alkalami.

” Duk lokacin da ka Fadi gaskiya a Kwankwasiyya sai ace maka kai ba mai biyayya ba ne ko ace maka batulu ne kai, don haka na ga dacewar na fice daga kungiyar ta Kwankwasiyya”.

Dan majalisar ya bayyana ficewar tasa ne a wata ganawa da ya yi da Freedom Radio Kano.

Talla

Ya ce ya fahimci duk da gudunmawar da suka bayar wajen samun narasa a zabukan da suka gabata Amma yanzu ana yi musu kallon bare.

” Da mu akai duk abun da aka yi har aka ci zabukan a Shekarar 2023, amma tun bayan zaben idan an zo za a raba Wani abu a gwamnatin sai a rika cewa mu ba yan asalin Kwankwasiyya ba ne, ko da yake dama na taba ji jagoran Kwankwasiyyar yana cewa kana bukatar kowa kafin ka ci zabe, amma idan ka ci kuma sai ka nemo naka”. Inji Hamza Massu

Kungiyar Dillalan Man Fetur Ta Nigeriya ta Cimma Matsaya da Matatar Mai ta Ɗangote

Ya ce daga yau a sani ya bi iyayen gidansa su Kabiru Alhassan Rurum da Sanata Kawu Sumaila wajen fice daga tafiyar Kwankwasiyya, kuma yace duk hukuncin da za a yiwa Rurum da Sanata Kawu to Kar a manta da shi shima a saka shi a cikinsu wajen hukuncin.

Hon. Hamza Massu ya ce yana nan a jam’iyyar NNPP amma mai kayan marmari ba mai littafi da alkalami ba.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a makon da ya gabata Kabiru Alhassan Rurum da Aliyu Sani Madakin Gini sun bayyana ficewarsu daga cikin kungiyar Kwankwasiyya wacce Rabi’u Musa Kwankwaso ke yiwa jagoranci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...