Ku janye yajin aiki, zan hukunta duk wanda aka samu da laifi – Gwamnan Kano ga Likitoci

Date:

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusif, ya roki kungiyar Likitoci ta jihar Kano ta janye yajin aikin da ta fara a daren jiya, gudun jefa rayuwar Milyoyin al’umma cikin hadari.

Gwamnan ya sanar da hakan ne, ta cikin wani shirin Kai-tsaye da ya yi da wasu kafafen yada Labarai a Gidan Gwamnatin jihar a daren jiya, inda ya ce zai dauki matakin da ya dace da zarar Kwamitin da ya kafa ya mika masa rahoton sakamakon binciken.

Talla

A cewar Abba, “Ina kira ga kungiyar Likitoci ta jihar Kano ta janye yajin aikin da ta fara, gudun jefa rayuwar al’ummar jihar sama da Milyan 20 cikin hadari”.

Ya kuma ce kamata yayi kungiyar ta jira taga matakin da Gwamnatin sa za ta dauka da zarar sakamakon binciken ya fito, maimakon tsunduma yajin aiki wanda zai tsaida dukkan ayyukan tallafawa marasa lafiyar dake matukar bukatar taimako.

Rikicin Abba da Kwankwaso: A karon farko Gwamnan Kano ya magantu

Ya kuma nemi afuwar su dangane da faruwar lamarin a madadin Gwamnatin Kano, inda yayi fatan zasu janye yajin aikin ko don Matan da suke Asibitin domin jiran haihuwa.

A karshe ya yi alƙawarin Gwamnatin sa za ta hukunta duk wanda aka samu da laifi a cikin lamarin, domin ya zama izina ga ‘yan baya.

Kungiyar Likitoci ta jihar Kano dai ta shiga yajin aikin ne bayan karewar wa’adin Awanni 48 da ta bawa Gwamnatin jihar, domin ta kori Kwamishiniyar Ma’aikatar Jin-kai ta jihar a sakamakon zargin cin zarafin wata mambar su dake aiki a Asibitin kwararru na Murtala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...