Kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar jihar Kano ta janye yajin aikin da suka fara a daren jiya, bayan Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ya sami nasarar sasanta rikicin dake faruwa, tsakanin kungiyar da kuma Kwamishiniyar Ma’aikatar Jin-kai ta jihar.
Shugaban Kungiyar Likitoci na jihar Kano Dakta Abdurrahman ne ya tabbatar da hakan, a yayin zantawar sa da manema Labaran a fadar Gwamnatin Kano.

Sanarwar da Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aiko wa jaridar kadaura24 ta ce yanzu haka likitocin sun koma bakin aiki domin ci-gaba da baiwa marasa lafiya cikakkiyar kulawar da suka saba.
Dakta Abdurrahman ya ce sun janye yajin aikin ne bayan wani zama na musamman da Gwamnan Kano, akan sabanin da aka samu a tsakanin Mambarsu da kuma Kwamishiniyar Ma’aikatar jin kai ta jihar kano.
Ku janye yajin aiki, zan hukunta duk wanda aka samu da laifi – Gwamnan Kano ga Likitoci
Ya kuma yaba wa Gwamnan a bisa gaggawar daukar matakin da ya kamata akan lamarin, harma yayi kira ga al’ummar jihar da su dinga bin dukkan hanyoyin da suka dace wajen shigar da korafin su akan jami’an lafiya domin a sami damar yin adalci ta hanyar bincika wa dama daukar matakin da ya kamata.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito an sami rashin jituwa tsakanin kwamishiniyar da wata likita wanda hakan yasa wasu daga cikin al’ummar jihar Kano sun goyi bayan kiran da Kungiyar likitocin ta yi na gwamnan Kano ya sauke kwamishiniyar daga mukaminta domin tana amfani da shi wajen cin zarafin al’umma.