Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusif, ya roki kungiyar Likitoci ta jihar Kano ta janye yajin aikin da ta fara a daren jiya, gudun jefa rayuwar Milyoyin alβumma cikin hadari.
Gwamnan ya sanar da hakan ne, ta cikin wani shirin Kai-tsaye da ya yi da wasu kafafen yada Labarai a Gidan Gwamnatin jihar a daren jiya, inda ya ce zai dauki matakin da ya dace da zarar Kwamitin da ya kafa ya mika masa rahoton sakamakon binciken.

A cewar Abba, βIna kira ga kungiyar Likitoci ta jihar Kano ta janye yajin aikin da ta fara, gudun jefa rayuwar alβummar jihar sama da Milyan 20 cikin hadariβ.
Ya kuma ce kamata yayi kungiyar ta jira taga matakin da Gwamnatin sa za ta dauka da zarar sakamakon binciken ya fito, maimakon tsunduma yajin aiki wanda zai tsaida dukkan ayyukan tallafawa marasa lafiyar dake matukar bukatar taimako.
Rikicin Abba da Kwankwaso: A karon farko Gwamnan Kano ya magantu
Ya kuma nemi afuwar su dangane da faruwar lamarin a madadin Gwamnatin Kano, inda yayi fatan zasu janye yajin aikin ko don Matan da suke Asibitin domin jiran haihuwa.
A karshe ya yi alΖawarin Gwamnatin sa za ta hukunta duk wanda aka samu da laifi a cikin lamarin, domin ya zama izina ga βyan baya.
Kungiyar Likitoci ta jihar Kano dai ta shiga yajin aikin ne bayan karewar waβadin Awanni 48 da ta bawa Gwamnatin jihar, domin ta kori Kwamishiniyar Maβaikatar Jin-kai ta jihar a sakamakon zargin cin zarafin wata mambar su dake aiki a Asibitin kwararru na Murtala.