Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir ya ƙaryata cewa akwai rigima ko wata matsala tsakaninsa da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso.
A cewarsa “mun yi shekaru 40 tare da Kwankwaso kuma ba wata rigimar da aka taɓa ji tsakaninmu, sai yanzu ne za mu yi hakan?”
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne jiya laraba yayin wata hira da ya yi a gidajen radio dake Kano.

Abba Kabir ya kuma ƙara da cewa ce-ce ku-cen rigimar siyasa ba shi ne a gabansa ba, illa yi wa jama’a aikin da zai amfane su.
APC Kano: Martani, Budaddiyar Wasika Zuwa ga Shugaba Tinubu – Daga Maikudi Lawan
Dangane da Kungiyar Abba tsaya da kafarka, gwamnan ya ce ba shi da alaka da ita, Sannan ya yi kira ga duk masoyansa da su gujewa furta kalmar ma ba wai shiga cikin kungiyar ko alaka da ita ba.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a yan kwanakin nan ana ta maganar cewa an Sami sabani tsakanin gwamnan da mai gidansa sanata Kwankwaso, wanda hakan yasa wasu suka kafa wata kungiya mai suna “Abba tsaya da Kafarka”.