Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya ki bin umarnin uban gidan sa Sanata Rabi’u Kwankwaso na cire wasu manyan jami’an gwamnati, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar rikici.
Mutanen da Kwankwaso ke son a tsige su, kamar yadda NAN ta ruwaito, sun hada da Kwamishinan Yada Labarai, Baba Dantiye, da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr Abdullahi Bichi.
Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillacin labarai NAN a ranar Talata cewa Kwankwaso bai ji dadin zargin Bichi na kin karbar umarni daga wajensa ba wajen gudanar da wasu ayyukansa .
NAN ta tattaro cewa jagoran jam’iyyar NNPP na kasa yana son a maye gurbin Dantiye da wani dan soshiya midiya wanda yake ganin ya fi cancantar tafiyar da ma’aikatar da kuma kare martabar gwamnatin jihar.
Sanata Kawu Sumaila ya zargi yan majalisa da daukar nauyin shaye-shayen matasa
Majiyoyin da ke kusa da gwamnan sun ce gwamna Yusuf ya gwammace ya tattauna da Kwankwaso kan lamarin maimakon ya yi aiki da ‘umarnin nasa.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ce wata kungiya ta bulla a Kano mai suna “Abba Tsaya Da Kafarka” Mai rajin Abba ya ya bijirewa uban gidansa”.
Rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta yi imanin cewa Kwankwaso ne ya zabo mafi yawan masu rike da mukaman siyasa na gwamnati da suka hada da kwamishinonin da dai sauransu .
Binciken NAN ya kuma gano cewa ‘yan majalisar tarayya na jam’iyyar NNPP kwanan nan sun gana da Yusuf inda suka bukace shi da ya tabbatar da ‘yancin kan sa.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban NNPP na jihar Kano Hamisu Dumgurawa ya sanar da dakatar da sakataren gwamnatin jihar kano Baffa Bichi da kuma kwamishinan sufuri Muhammad Doggon daga jam’iyyar.
Ya ce an dakatar da su ne bisa zargin cin zarafin jam’iyya.
Da NAN ta tuntubi Kwankwaso ya ki cewa komai game da lamarin, sai ya ce: “Ba zan ce komai akan wannan batun ba tunda shugaban jam’iyyar ya riga ya dauki matakin da ya dace.