Sanata Kawu Sumaila ya zargi yan majalisa da daukar nauyin shaye-shayen matasa

Date:

Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta kudu a majalisar dattawa, ya zargi ƴan siyasa, musamman ƴan majalisa da ƙarfafa shaye-shayen ƙwayoyi a tsakanin matasa.

Ya ce ƴan siyasa suna sayo wa matasan ƙwayoyi, sannan suna ƙarfafa musu gwiwar ta’ammuli da su domin samun damar yi musu dabar siyasa musamman a lokacin zaɓe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Talla

Kawu Sumaila ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake nasa bayanin a kan ƙudurin da Sanata Rufa’i Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya ya gabatar, mai taken, “dokar kafa cibiyar hana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da gyara tunanin mashaya da sauran abubuwa masu alaƙa,” a ranar Talata.

Talla

“Yanzu da nake wannan maganar, yawancin ofisoshinmu da gidajenmu ba za a rasa ƙwayoyi ba,” in ji Kawu.

“Na san wasu jagororin siyasa da suke ƙarfafa gwiwar masu shaye-shaye a Najeriya. Don haka akwai buƙatar mu ɗauki wannan batu da muhimmanci.”

Talla

Ya ƙara da cewa, “mutum nawa ne a cikinmu za su iya rantse wa Ƙur’ani ko Baibul cewa ba sa ƙarfafa wa masu shaye-shaye a mazaɓunsu?”

A ƙarshe ya yi kira da a riƙa yin gwajin shaye-shaye ga duk wani wanda yake son tsayawa takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...