Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Jam’iyyar NNPP dake mulkin jihar kano ta dare gida biyu, sakamakon bullar wani tsagi dake da’awar su ne halastattun shugabannin jam’iyyar a jihar.
Barista Dalhatu Shehu shi ne wanda ya bayyana Kansa a matsayin sabon halastaccen shugaban jam’iyyar NNPP na jihar kano, ya ce su uwar jam’iyyar ta kasa ta sani a matsayin shugabanninta a jihar.
” Mu masu jam’iyyar wadanda suke da satifiket din jam’iyyar suka yarda da mu a matsayin shugabanninta, kuma mu har yanzu kwandon kayan marmari shi ne alamar jam’iyyar mu , ba littafi da alkalami ba”. Inji Barr Dalhatu
Ya ce tuni sun Kori Kwankwaso da mukarrabansa daga jam’iyyar don haka suke kira a garesu da kasa su sake bayyana kansu a matsayin yan jam’iyyar. Ya kuma ba da tabbacin tuni suka shirya shiga zaɓen kananan hukumomin jihar kano da za a gudanar a wannan watan.
Abba tsaya da kafarka: Sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu
” Kamar yadda kowa ya sani za a yi zaɓen kananan hukumomin Kano a ranar 26 ga watan October, tuni mun turawa hukumar zabe ta Kano sunayen wadanda za su yi mana takara a zaben, amma mun fahimci ita hukumar zaɓen tafi fifita sunayen wadanda Kwankwaso ya tura musu”. Inji Barr Dalhatu Shehu
Ko da aka tutunbi shugaban jam’iyyar NNPP tsagin Kwankwasiyya Sulaiman Hashim Dungurawa yace ba su da labarin bullar sabbin Shugabannin, amma yace yana zargin yan adawa ne suke kokarin hura musu wutar rikici a jam’iyyar.
” Wasu yan adawa ne suke zuga su, amma zamu dauki matakin da ya dace akansu, idan muka fahimci abun nasu da gaske ne, amma idan muka ga shiririta ce abun nasu to zamu rabu da su kawai”.
A Yan Kwanakin nan dai jam’iyyar NNPP ta fada cikin rikici tun lokacin da aka samar da wata kungiyar mai suna Abba tsaya da kafarka, wadda kuma aka zargi Sakataren gwamnatin jihar kano Dr. Baffa Bichi da daukar nauyin kungiyar.
Sai dai bayan jam’iyyar NNPP tsagin su Dungurawa ta ce ta dakatar da sakataren gwamnatin daga Jam’iyyar, Baffa Bichin ya fi ya nesanta kansa da waccen sabuwar kungiyar.