Abba tsaya da kafarka: Sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Abdullahi Baffa Bichi ya nisanta kansa daga zargin da ake masa na jagorantar kungiyar Abba-Tsaya-da-kafarka.

Alhaji Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana haka ne Jim kadan bayan da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci sulhunta tsakanin sakataren gwamnati da Alhaji Hamza Maifata a gidan gwamnati.

Talla

” Ni Jarumi ne ba wanda nake tsoro dani na kafa kungiyar da zan fito na fadawa duniya, domin a duk duniya yanzu ba wanda nake tsoro”. Inji Baffa Bichi

Alhaji Abdullahi Baffa Bichi Wanda ya jaddada biyayyarsa ga gwamna Abba Kabir Yusuf yace zai ci gaba da biyayya ga gwamnatin Kano da jamiyyar NNPP.

Yadda Gwamna Yusuf ya tasamma warware rikicin cikin gida da ya taso a NNPP Kano

A nasa bangaren Dantakarar shugabancin karamar hukumar Bichi Alhaji Hamza Maifata Bichi ya ya bayyana gamsuwarsa da sulhun da aka yi tare da alwashin wani sabani ba zai Kara shiga tsakaninsu ba a nan gaba.

Talla

A nasa shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano. Alhaji Lawan Hussain Chediyar Yangurasa ya ce wasu makiya Jam’iyyar jihar Kano ne suke kokarin haddasa rikici a jihar Kano domin biyan bukatun Kashin kansu.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a Kwanakin nan ne dai wata kungiya ta bulla mai suna Abba tsaya da kararka wadda aka zargi Sakataren gwamnatin da daukar nauyin kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...