Kungiyoyin APC a Kano ta Arewa sun yi watsi da Barau, Ganduje zuwa NNPP na Kwankwaso

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Kimanin kungiyoyi sama da 23 daga Kano ta Arewa suka yi watsi da jam’iyyar APC suka koma jam’iyyar NNPP ta hannun Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Daga cikin kungiyoyin akwai kungiyar Askarawan Gandujiyya ta Kano ta arewa wadda dukkanin mambobinta daga kananan hukumomi 11 cikin 13 da ke yankin suka koma NNPP.

Shugaban kungiyar, Sale Musa Romo ne ya sanar da sauya shekar, ya bayyana cewa tsarin siyasarsu wanda ya kunshi mutane 11,111 ya ruguje zuwa jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso .

Talla

A cewar Romo, sun dauki matakin ne sakamakon cin amanar da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa suka yi musu kuma dukkaninsu sun fito daga shiyyar Kano ta arewa.

“Mun zo nan ne domin mu narkar da tsarinmu, mu shiga cikin takwarorinmu na Askarawan Kwankwasiyya, a jam’iyyar NNPP,” in ji Romo, tare da hada kan kungiyarsa da tafiyar siyasar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rikicin NNPP: Kar ka saka ni a abun da bai kamata na shiga ba – Kwankwaso

Daga cikin kungiyoyin har da APC G7, kungiyar da Sanata Barau yayi amfani da ita wajen kalubalantar Ganduje a 2022.

Sauran kungiyoyi irin su Barau Kafa da Kafa, APC Hunters Vanguard, Barau Enlightenment and Strategy, suma duk sun koma jam’iyyar NNPP.

Rikicin PDP: Gwamnonin PDP sun bayyana Matsayarsu

Da yake karbar wadanda suka sauya shekar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takarar shugaban kasa a 2023, ya bayyana jin dadinsa da karbar dimbin ‘yan jam’iyyar ta APC.

Talla

“Na yi farin ciki da kuka baro wancan tsarin na APC yanzu kuma kuka shigo jam’iyyar da ake yi wa kallon aljannar siyasa ga talakawa,” inji Kwankwaso.

Wannan al’amarin ya nuna gagarumin koma baya da jam’iyyar APC take samu a Kano ta Arewa, yayin da jam’iyyar NNPP ke ci gaba da kara karfi a siyasar yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...