Kamaru ta buɗe Madatsar Lagdo: Jihohin 11 Najeriya su shirya wa ambaliya —Gwamnatin Nigeria

Date:

Hukumar Albarkatun Ruwa ta Najeriya (NIHSA) gargaɗi ’yan ƙasar game da yiwuwar samun ƙarin ambaliya a wasu yankuna bayan da ƙasar Jamhuriyyar Kamaru ta sako ruwa daga Madatsar Ruwa ta Lagdo.

Darakta-Janar na Hukumar NIHSA, Umar Mohammed, ya sanar cewa a ranar Talata Kamaru ta bude dam ɗin Lagdo — a daidai lokacin da ambaliya ta yi barna sosai a sassan Najeriya.

Ta baya-bayan na ita ce ta Maiduguri, wadda ta shafi sama da mutane miliyan daya ta shanye kashi uku bisa hudu na birnin.

Ambaliyar Ruwa: Sarki Aminu Bayero ya jajantawa al’ummar Maiduguri

Umar Mohammed ya ce hukumarsa za ta riƙa lura da yanayin tafiyar ruwan Madatsar Ruwa ta Lagdo, domin sanar da ’yan Najeriya inda aka kwana domin guje wa ambaliya.

A cewarsa, duk da cewa babu alamar samun babbar ambaliya a Najeriya a sakamakon hakan, amma ya kamata hukumomi da gwamnatoci a dukkan matakai su kasance cikin kyakyyawan shirin ko-ta-kwana.

Ya jaddada cewa jihohin da ya kamata su kasance cikin shiri sosai domin kauce wa tasirin ruwan Madatsar Ruwa ta Lagdo da za a sako su ne: Adamawa, Taraba, Kogi, Nasarawa, Binuwai, Anambra, Bayelsa, Delta, Edo, Kuros Riba da kuma Ribas.

Lagdo wata katafariyar madatsar muwa ce da ke Arewa Jamhuriyar Kamaru, da ke turo ruwa zuwa Kogin Bibuwai, mai faɗin 586km2.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta bayyana cewa ruwan Madatsar Ruwa ta Lagdo da aka sako a 2022 ya haddasa mummunar ambaliya a Najeriya, wafda ta kashe mutane 693, ta raba miliyan 1.4 da gidajensu.

Mutane 2,400 kuma sun jikkata bayan ga gidaje 82,035 da gonaki masu faɗin hekta 332,327 da ta lalata.

Iftila’i: Yara hudu sun mutu a cikin firinji

A 2023 ma an samu irin haka, lamarin da hukumar NIHSA ta zargi gwamnatin Kamaru da rashin sanar da da Najeriya, sai bayan kwanaki bakwai da bude dam ɗin.

A watan Oktoba 2023 Majalisar Dattawa ta umarci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ta sake waiwayar aikin gina Madatsar Ruwa ta Dasin Hausa da sauran madatsun ruwa da za su taimaka wajen ɗauke ruwan da Kamaru take sakowa daga Madatsar Ruwa ta Lagdo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...