Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana ibtila’in ambaliyar ruwan da aka samu a Maidugurin jihar Borno da cewa wani babban abu ne da ya girgiza al’umar Kasar nan baki daya.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a sakonsa na jajantawa al’umar jihar Borno da Kasa baki daya bisa ambaliyar ruwan data faru a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Iftila’i: Yara hudu sun mutu a cikin firinji
Yace ba kasafai aka fiya samun irin wannan mummunan ambaliyar ba, amma idan hakan ya faru to babu abunda ya kamata ga al’uma sai yin addu’ar Allah Kada ya sake maimatawa.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu ya kuma bada lafiya ga wadanda suka jikkata tareda mayar da mafificin alheri ga wadanda suka rasa dukiyoyinsu.
Daganan mai Martaba Sarkin ya sake Mika jajensa ga Shugaban Kasa chief Ahmad Bola Tinubu da Mataimakinsa Alhaji Kashim Shetima da Gwamnan jihar Borno Professor Baba Gana Umara Zulum da Shehun Borno Alhaji Mustapha El Garbai.