Wasu yara huΙu sun mutu lokacin da suke wasa a cikin wani tsohon firinji a yankin Zambezi da ke arewa maso gabashin Ζasar Namibia, inda tuni Ζ³ansanda su ka fara gudanar da bincike kan lamarin.
BBC ta rawaito cewa yaran masu shekara uku zuwa shida, an gano su ne a cikin firijin da aka daina amfani da shi a yankin mai cike da cunkoso a garin Katima Mulilo a jiya Litinin da yamma.
Rundunar βyan sandan ta yi imanin cewa yaran sun maΖale ne a lokacin da suke wasa, inda suka faΙa ciki, amma ana ci gaba da bincike.
Tinubu ya fi Ζarfin satar dukiyar Najeriya β Minista
Biyu daga cikin yaran sun mutu nan take a cikin firijin yayin da sauran biyu kuma suka mutu a asibiti lokacin da suke karΙar magani, kamar yadda kafafen yaΙa labarai a yankin suka ruwaito.
βLokacin da na shigo, na ga jami’an lafiya na kula da Ιiyata da wata yarinya. Sun garzaya da su asibiti, yayin da sauran biyun kuma aka saka su cikin motocin Ιaukar gawawwaki,β in ji Aranges Shoro, mahaifin yaran, akmar yadda ya shaida wa wata jaridar Ζasar ta Namibia.
An sanar da mutuwar sauran yaran biyu bayan garzaya da su asibitin Katima Mulilo da ke kusa, kamar yadda kafar yada labarai ta NBC ta ruwaito.