Daga Rukayya Abdullahi Maida
Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya yi kira ga Musulmin Najeriya da su yi koyi da karantarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a duk harkokinsu na yau da kullum.
Ministan ya yi wannan tsokaci ne a sakonsa na murnar zagayowar watan maulidin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, wanda babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi ya aikowa kadaura24.
Don haka Gwarzo ya hori musulmi da su yi riko da koyarwa tare da kwaiwayon manzon Allah mai tsira da amincin Allah, yana mai cewa hakan ne zai inganta rayuwar al’umma da kuma fitar da Nigeria daga tabarbarewar tattalin arzikin da take fuskanta .
Farashin Mai: Takaddama ta barke tsakanin Ɗangote da NNPC
A cewarsa “muna murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), amma ya zama wajibi ga dukkan musulmi su yi tunani a kan kyawawan dabi’unsa da koyarwarsa tare da yin koyi da shi a dukkan harkokinmu na yau da kullum”. “Kazalika mu rika koyi da koya da halinsa na tausayi, zaman lafiya da kaunar juna,” Ministan ya kara da cewa.
Maulidi: Murtala Sule Garo ya taya al’ummar Musulmi Murnar zagayowar watan haihuwar Annabi S A W
“Ci gabanmu ya ta’allaka ne da yadda muka aiwatar da koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da ke koyar da dan Adam yadda zai zauna da kowa lafiya, wajibi ne a kan musulmin Nijeriya su yi aiki bisa koyarwa da bin ka’idojin Musulunci don ci gaban al’umma kasar mu.”
Minista Gwarzo, ya kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su sake jajircewa wajen ganin shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kawo sauyi a kasar nan. Ya kara da cewa ma’aikatar gidaje da raya birane ta kuduri aniyar ganin kowane dan Najeriya ya samu gidaje masu rahusa.