Majalisar Wakilan Nigeria ta sha alwashi hukunta duk masu hannu a cin zarafin sojan nan Seaman Abbas

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin Rundunar Sojin Ruwa ya sha alwashin gudanar da bincike kan tsarewar da aka yi wa Seaman Abbas Haruna ba bisa ka’ida ba har na kusan shekaru shida, bisa umarnin wani Birgediya Janar MS Adamu, tare da yin alkawarin tabbatar da cewa an hukunta duk wadanda ke da hannu a cikin wannan lamarin.

Da take bayyana yadda lamarin ya faru, a cikin wani shirin ‘Berekete’ na gidan Talabijin na Human Rights, matar Seaman Abbas wato Hussaina Iliyasu ta ce an kulle mijin nata ne tun a shekarar 2018 a lokacin da aka tura shi aikin hadin gwiwa a Sarti Baruwa jihar Taraba, inda zai yi aiki karkashin rundunar Birgediya MS Adamu.

Tace an samu rashin fahimtar juna a tsakaninsu, lamarin da ya kai ga tsare shi a wani yanayi na rashin jin dadi na tsawon shekaru da dama ba tare da bin shari’ar da ta dace ba kamar yadda dokar soja ta 2004 ta Tarayyar Najeriya ta tanada.

Farashin Mai: Takaddama ta barke tsakanin Ɗangote da NNPC

A Wata sanarwa da shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin Rundunar Sojin ruwan Nigeriya Yusuf Adamu Gagdi, ya ce ba zasu barim wannan cin mutuncin da aka yi wa Seaman Abbas kan wata ‘yar rashin fahimta da mai gidansa ta tafi a banza ba.

Lamarin dai ta tashi hankulan al’umma da dama a Nigeria musamman ga wadanda suka kalli yadda matar Seaman Abbas ta rika ba da labarin irin cin zarafin da aka yi masa wanda har ta kai ga ya haukace.

Maulidi: Minista T Gwarzo ya bukaci al’ummar Musulmi su rika koyi da halayen Annabi S A W

Matsakaicin rashin imanin da Birgediya Janar MS Adamu ya nuna wa na karkashinsa kan wani dan karamin lamari, ya jawo kakkausar suka daga miliyoyin ’yan Najeriya masu hankali da suka ji labarin.

Labari mai ban tausayi na Seaman Abbas Haruna, wanda aka sanyawa kafar yada labarai ta ‘Berekete’ ya sa kwamitin majalisar wakilai kan harkokin ruwa ya shiga cikin lamarin da nufin bayyana gaskiya da kuma kare mutuncin sojojin mu da hakkin kowane mutum a karkashinsa.

Bugu da kari, “zamu bi duk matakin da ya dace da dokokin aiki soji domin ganin duk jami’an da abin ya shafa ya fuskanci hukunci daidai da abun da suka yin”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...