Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar watan Maulidi.
12 ga watan Rabi’ul Awwal ita ce ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Wanda musulmi ke murna da samuwar sa ta hanyar shirya karatuttuka da zumunci da liyafar cin abinci da kasidu ga daliban makarantun Islamiyya.
Murtala Sule Garo yi kira ga dukkan masu rike da madafun iko a kowanne mataki da su duba Allah su kawo tsarin da zai saukakawa al’umma halin da su ke ciki.
Farashin Mai: Takaddama ta barke tsakanin Ɗangote da NNPC
Tsohon kwamishinan kananan hukumomin yai kira mahukunta da su yi dukkan mai yiwuwa dan inganta tsaro a Nigeria.
NNPC ya fitar da farashin da yan Nigeria za su rika sayan man fetur din Ɗangote
Ya ce, “Ina kira ga al’umma Musulmi da su dage da addu’a musamman a wannan wannan watan na Maulidi akan harkar tsaro da kuma daba da ta addabi al’umar jihar Kano.
“Ina kira da mahukunta da kyautata rayuwar Almajirai da samawa matasa aikin yi. Ta wannan hanya ce za a iya inganta rayuwar al’umma.”
Ina kuma kira ga al’ummar musulmi da suyi anfani da tarukan mauludi wajen yin adduo’in samun zaman daya da saukin rayuwa a jihar Kano da Najeriya baki daya.