Abubunwan da ya kamata ku sani game da farashi da fitar da man fetur din Ɗangote

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta baiwa Sarki Aminu sabon Umarni

Matatar man Dangote ta shirya yin tasiri sosai a kasuwar man Najeriya, inda za a fara rabon mai a ranar 15 ga Satumba, 2024.

Jerin sunayen yan takara 38 da NNPP ta tsayar a zaɓen shugabannin kananan hukumomin Kano

Majiyar Kadaura24 ta daily news24 ta lura da cewa ana sa ran matakin zai yi tasiri ga farashin man da da kuma wadatar man fetur din a fadin Nigeria.

A Daily Post, ta rawaito cewa ana sa ran farashin man fetur din na matatar Dangote zai kasance tsakanin N857 zuwa N865 kowace lita a gidajen mai.

 

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) zai sayi man fetur daga matatar a kusan N840 zuwa N850 kowace lita, tare da nuna cewa NNPC na iya ba da wani tallafi don man ya zama mai araha ga masu amfani.

Jaridar Punch ta rawaito wannan farashin ya nuna cewa za a sami rage daga kudin da ake sayan man a yanzu wanda ya fara daga N900 zuwa N1,200 a kowace lita, ana kuma sa ran farashin zai iya kara daidaita nan da Oktoba 2024, lokacin da ake sa ran Dangote zai sami ƙarin iko a kan farashin man a kasuwa.

Fito da man domin Rarrabawa

Domin magance matsalar karancin man fetur da ake fama da shi, hukumar NNPC ta hada manyan motoci 300 domin fara jigilar mai daga matatar Dangote. Rahotanni da jaridar Punch sun tabbatar da cewa matatar man na shirin raba lita miliyan 25 na man fetur a kullum domin saukaka matsalar ƙarancin man a fadin Najeriya.

Kalubalen da ke gaba

Wasu ‘yan kasuwar man sun yi shakkun sayen man fetur daga matatar man ta Ɗangote. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa kamfanin na NNPC ya fara tattaunawa da ‘yan kasuwar don nusashe da su.

‘Yan Najeriya dai na fatan karin man daga matatar Dangote da aka samu zai taimaka wajen daidaita farashin man fetur din da kuma wadatuwar man a fadin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...