Daga Rukayya Abdullahi Maida
Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin wucin gadi na hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero gyaran karamar fadar Nasarawa.
kotun ta bayar da umarnin kar a sauya ko jirkita fasalin gidan har sai ta saurari karar da kuma yanke hukunci.
Sojojin Nijeriya sun sake hallaka kasurgumin dan fashin daji a Katsina
kazalika kotun ta bayarda umarnin sadar da sarki Aminu da umarnin nata, tare da sanya ranar 2 ga Oktoba don sauraron karar da Matawallen Kano, Alhaji Ibrahim Ahmed ya shigar.
Da dumi-dumi: Gwamnatin Kano ta sake chanza ranar komawa makarantun firamari da sakandire
Idan za’a iya tunawa Sarkin na 15 ya bayyana aniyarsa ta sake gyara gidan sarki na Nasarawa, Inda har aka fitar da taswirar yadda gidan zai kasance idan an kammala gyaran.