Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta sake chanja ranar komawa makarantun firamari da sakandire zuwa ranar Talata 17 ga Satumba, 2024.
Yayin da daliban makarantun kwana a fadin jihar za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.
Wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, ta ruwaito kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa yana bayyana cewa chanja ranar komawa makarantun tana da nasa da yadda gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 16 ga watan Satumba, 2024 a matsayin ranar hutu domin bikin Mauludi.
Sojojin Nijeriya sun sake hallaka kasurgumin dan fashin daji a Katsina
“Saboda haka an chanja ranar ne domin baiwa dalibai damar gudanar da bukukuwan maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Sojojin Nigeria sun Kashe Ƙasurgumin Dan ta’adda da ya addabi Arewacin Nigeria
“A yayin da nake taya al’ummar Musulmi murna, ina kira gare su da su rungumi dabi’ar hakuri, sadaukarwa, da kishin kasa tare da ci gaba da yi wa jihar kano addu’a da kasa baki daya,” inji shi.
Don haka sanarwar ta bukaci iyaye da dalibai da su lura da sabuwar ranar da za a ci gaba da aiki don tabbatar da daliban sun koma makarantunsu kamar yadda aka sanya.