Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammdu Sanusi II, ya yi alƙawarin taimakawa kwamitin tabbatar da tsaron unguwar Ɗorayi da kewaye domin magance matsalar tsaron da ta dade tana addabar al’ummar yankin.
Sarki Sanusi ya bayyana hakan ne a yayin da ya karɓi baƙuncin kwamitin yankin a fadarsa, inda ya ce Masarautar za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalar tsaron.
Haka kuma Sarki Sanusi ya ƙara da cewa, yana matuƙar tausayawa al’ummar yankunan da matsalar take damu, duba da irin illolin da hakan ke haifarwa.
Malam Abdullahi Idris Ɗan fodiyo yana cikin iyayen kwamitin tsaron na unguwar ta Dorayi da kewaye, ya yi wa Sarkin cikakken ƙarin haske akan matsalar tsaron da ta addabi yankin wadda take neman sabauta rayuwar su.
Zaɓen Kano: NDLEA ta fitar da sakamakon yan takara 20 da aka yiwa gwajin shan kwaya
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan da fitowa daga masarautar, Ɗan Fodiyo ya bayyana ƙoƙarin da masana’antun Kano suke yi musu wajen magance matsalar tsaron yankin.
A ƙarshe dukkan ɓangarorin biyu sun yi fatan samun zaman lafiya a jihar Kano dama ƙasa baki-ɗaya.