Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gidan ajiye namun daji na jihar Borno ya nuna damuwa da bisa yadda ambaliyar ruwa ta shigar da muggan dabbobi a cikin al’ummar jihar .
Babban Manajan Gidan ajiye namun dajin na jihar Borno, Ali Abatcha Don Best, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata.
Rabon tallafin a Kano: APCn Kano ta Caccaki Kwankwaso
Ya ce bala’in ambaliya ya yi sanadiyyar asarar dukiyoyi da kuma mutuwar sama da kashi 80% na dabbobin da suke da su.
Babban manajan gidan namun dajin ya ba da tabbatar zasu iya bakin kokarinsu wajen ganin sauran dabbobin ba su fice daga gidan ba.
“Daga karshe, ya yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa daga Allah Madaukakin Sarki kuma ya kira dukkan al’ummar jihar da su yi addu’a su koma ga Allah Madaukakin Sarki,” in ji sanarwar.
Daily Trust