Daga Sani Idris Maiwaya
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta caccaki jigon jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kan yadda ya soki tsarin da gwamnatin tarayya ta bi wajen rabon kayan tallafin abinchi domin ya kai ga mabukata.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Sanata Kwankwaso ya kalubalanci tsarin gwamantin tarrayya na baiwa jagororin jam’iyyar APC damar jagorantar rabon kayan tallafin abinchi da aka turo arewa maso yammacin Nigeria har da jihar kano.
A sanawar da Kwankwaso ya fitar jiya litinin ya yi zargin cewa an baiwa kowanne gwamna a Nigeriya ya raba tallafin amma a Kano sai aka baiwa yan Jam’iyyar APC , Inda ya ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulki da tsarin dimokaradiyya.
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje a Maiduguri
A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na jihar kano Alhaji Abdullahi Abbas ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen rage yunwa a kasar nan, amma gwamnatin NNPP na kawo cikas ga yunkurin.
Ya ce, shugaba Tinubu ya amince da wasu matakan da za su taimaka wa talakawa marasa galihu, amma mutanen da aka ware domin rabon tallafin a baya suna karkatar da shi.
Abbas ya yi nuni da cewa, badakalar karkatar da kayan tallafi ta mamaye manyan jami’an gwamnatin NNPP, wanda hakan ta sa tallafin bayan isa ga talakawan da ake ba da tallafin domin su.
Abbas ya ce, bayan zarge-zargen baya, kwanan nan sai da aka sami wani kaso mai yawa na shinkafa da ake son rabawa talakawa a gidan shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi, wanda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ke binciken lamarin.
“Ka fadawa gwamnan Kano ya fito ya yiwa al’ummar jihar bayani dalla-dalla kan tallafin da gwamnati tarayya ta rika turo masa, idan yayi bayani sai ka zo ka fara korafi”. A cewar Abdullahi Abbas
Don haka sanarwar ta yi kira ga Kwankwaso da ya shaida wa gwamnansa da ya kaddamar da bincike kan wadannan zarge-zargen tare da gurfanar da wadanda aka samu da laifi a gaban kotu don hukuntasu.
Rabon Tallafi a Kano: Kwankwaso ya koka wa shugaba Tinubu
Abbas Kwamitin da gwamnatin tarayya ta sake nada yana karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, Sannan ya kunshi mambobin jam’iyyar APC dana NNPP da PDP. Sanata Rufa’i Hanga (NNPP), Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila (NNPP), ‘yan majalisar wakilai, Kwamared Aminu Abdussalam, mataimakin gwamnan jihar, shugabannin gargajiya da na addini, da dai sauransu duk suna cikin kwamitin rabon kayan tallafin na Kano.
Abbas ya ce kwamitin da ya kunshi yan jam’iyyu biyu shi ne ya zauna ya fitar da yadda za a tara tallafin ba tare da an Sami wasu sun karkatar da tallafin ba.
Dangane da batun nade-naden daraktocin hukumar DSS kuwa, shugaban APCn ya ce mataki ne da Shugaba Tinubu ya dauka domin baiwa jihar kano kulawa ta musamma da kuma nada hazukai wadanda zasu kula da tsaron Kano.
Ya lura cewa a tsawon mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Shekaru 8, Kano ta kasance cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba.
Ya kara da cewa, “Tashin hankali da ake fama da shi a jihar, gwamnatin NNPP ce ta haifar da shi, domin ta karfafawa matasa masu tada zaune tsaye, tare da tallafa musu.