Mafi Ƙarancin Albashi: Majalisar dokokin Kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kuɗi na N99b

Date:

 

 

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kwarya kwaryar kasafin kudi na Naira Biliyan 99 domin baiwa gwamnatin jihar damar aiwatar da mafi karancin albashi da wasu ayyukan.

Shugaban majalisar dokokin, Alhaji Jibril Falgore, ya ce kasafin zai baiwa gwamnatin jihar damar biyan mafi karancin albashin da kuma gudanar da ayyukan raya kasa.

Sannan ya godewa ‘yan majalisar saboda amincewa da kasafin ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnatin tarayya ta fara sayar da shinkafarta akan Naira 40,000

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa a ranar 27 ga watan Agusta ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aikewa majalisar kwarya kwaryar kasafin na Naira Biliyan 99.

Man Fetur shi zai rika yiwa kansa farashi yanzu a Nigeriya – NNPC

Tun bayan sanya hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashi na Naira dubu 70, jihohi da dama suka fara kafa kwamitin aiwatar da kasafin.

Jihar Adamawa ce dai, ta zamo ta farko wajen fara biyan mafi karancin albashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...