Badakalar magunguna: Abubunwan da muka gano bayan kama Dan Kwankwaso da wasu mutum 4 – Muhuyi Magaji

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hukumar karbar korafe-korafen da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da suka hada da Alhaji Mohammed Kabara, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu bisa badakalar bada kwangilar magunguna na biliyoyin naira.

Haka kuma hukumar ta kama shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin Najeriya (ALGON) reshen jihar, Alhaji Abdullahi Bashir, wanda kuma shi ne kantoman karamar hukumar Tauroni .

Hakazalika, hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta damke Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Novomed, Garba Kwankwaso, wanda dan dan uwan jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sen. Rabi’u Kwankwaso, kan badakalar da ake zarginsa da aikatawa.

Da dumi-dumi: Ogan Boye ya ajiye mukaminsa na Mai baiwa gwamnan Kano shawara Kan Matasa

Ana dai zargin wadancan mutane ne da hada baki wajen bai wa kamfanin Novomed kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomin jihar 38, wanda hakan ya saba wa dokokin sayo kayayyakin gwamnati.

Bincike ya nuna cewa kowanne daga cikin kananan hukumomin 38 ya biya Novomed Naira miliyan 9.150 domin siyan magunguna amma ba a kawo musu magunguna ba.

“Muna da kananan hukumomi 44 a jihar kuma sun yi nasarar karbar Naira 9.150 daga kananan hukumomi 38 domin samar da magungunan da ba a kawo su ba.

“Binciken ya kuma nuna cewa dukkan wadanda ake zargin suna ba mu hadin kai wajen gudanar da binciken “, wata majiya da ke cikin hukumar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

Badakalar magungunan Kano: Mun fara bincike kuma za mu gurfanar da duk mai hannu – Muhuyi Magaji

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Kabiru Kabiru ya tabbatar da kamen, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Kabiru ya ce hukumar na kokarin bankado yadda aka gudanar da zamban tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kuliya.

Ya kuma tabbatar da cewa wadanda ake zargin suna hannun hukumar har zuwa lokacin hada da wannan rahoto.(NAN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...