Daga Isa Ahmad Getso
Jam’iyyar APC reshen jihar kano ta nada Ibrahim Soja Kantin Kwari a matsayin sabon shugaban kungiyar APC Media Forum Gawuna Garo.
Ida za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito kungiyar ta shiga cikin ruɗani ne tun lokacin da tsohon shugaban kungiyar Aminu Black Gwale ya umarci ‘ya’yan Kungiyar da su dakata daga kare jam’iyyar APC da jagororinta na jihar kano.
Wadancan kalamai sune suka yi Sanadiyar Aminu Black Gwale ya rasa kurarsa, kuma bayan sauke shi an nada Hon. Ibrahim Soja Kantin Kwari a matsayin sabon shugaban kungiyar APC Media Forum Gawuna Garo.
Badakalar magunguna: Abubunwan da muka gano bayan kama Dan Kwankwaso da wasu mutum 4 – Muhuyi Magaji
Sakataren jam’iyyar APC na jihar kano Hon. Ibrahim Zakari Sarina ne ya jagoranci rantsar da Ibrahim Soja a matsayin sabon shugaban kungiyar APC Media Forum Gawuna Garo.
Sabon shugaban dai zai rike Shugabanci kungiyar ne a matsayin Shugaban riko kafin daga bisani a gudanar da zabe.
Da yake jawabi bayan karbar rantsuwar kama aiki, Ibrahim Soja ya godewa shugabannin jam’iyyar APC na jihar kano bisa goyon bayan da suka bashi har ya zama Shugaban kungiyar.
Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APCn Kano
” Ina ba ku tabbacin zan tsaya tsayin daka don ganin ya’yan wannan kungiya sun kare kima da martabar jam’iyyar ta APC da kuma jagororin mu masu daraja”. Inji Soja Kantin Kwari
Ya ce zai yi duk mai yiwuwa don ganin ya’yan wannan kungiya sun sami hakkokinsu tare da samar musu da walwala, don samin nasarar da aka sanya a gaba.