Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban kasa Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea a ranar laraba 14 ga watan Agusta a wata ziyarar aiki ta kwanaki uku
Tinubu zai je kasar ne domin girmama gayyatar da shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya yi masa.
Dalilin da ya haifar da rikici tsakanin yan bindiga har suka kashe 30 daga cikinsu
Tinubu, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, zai gana da shugaban kasar Equatorial Guinea a fadar shugaban kasar idan ya da isa, inda za a yi taruka tsakanin shugabannin biyu da kuma kulla yarjejeniyoyin da suka shafi man fetur da iskar gas da kuma tsaro.
Zargin karkatar da shinkafa: EFCC ta karɓi korafi kan shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano
Shugaban Najeriyar dai zai samu rakiyar ministan harkokin wajen kasar Ambasada Yusuf Tuggar da sauran mukarraban gwamnatinsa, wadanda za su sa hannu wajen rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da kuma nazarin damarmakin inganta alakar da ke tsakanin kasashen biyu.