Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaba Bola Tinubu yanzu haka na jagorantar taron majalisar kasa, wadda ta kunshin tsofaffin shugabannin Nigeria a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Taron wanda shi ne irinsa na farko a tun bayan rantsar da shugaba Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023, taron yana gudana ne a zauren majalisar tare da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Taron wanda aka fara da karfe 12:27 ya sami halartar taron tsoffin shugabannin kasa, Janar Abdulsalam Abubakar da Yakubu Gowon ta na’urar gani ga ka.
Zargin karkatar da shinkafa: EFCC ta karɓi korafi kan shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ba su halarci taron ba.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio; Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da wasu Gwamnonin Jihohi da Mataimakan Gwamnoni.
Taron farkon dai ana sa ran zai tattauna halin da al’ummar kasar ke ciki musamman kalubalen tattalin arziki da al’ummar kasar ke fuskanta.
Da dumi-dumi: Gwamnatin Kaduna ta janye dokar hana fita
Majalisar wadda kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 ya amince da ita, tana taka muhimmiyar rawa wajen bayar da shawarwari a cikin harkokin mulkin kasa.
Majalisar wadda ta kunshi shugaban kasa a matsayin shugaba da mataimakin shugaban kasa a matsayin mataimakin shugaban majalisar, ta kuma kunshi dukkanin tsofaffin shugabannin kasa da shugabannin kasa, da dukkan tsofaffin alkalan Najeriya, shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, gwamnonin jihohi da lauyoyi da Janar- janar na kasa.