Babban Hafsan Tsaro (CDS), Christopher Musa, ya ce sojoji za su shigo ciki idan zanga-zangar ‘#EndbadGovernance’ da ke ci gaba da gudana a fadin kasar ta ci gaba da rikide wa zuwa tashin hankali.
Musa dai na mayar da martani ne kan barna da sace-sace da aka yi a zanga-zangar da aka yi a sassa da dama na kasar a ranar Alhamis.

Ko a ranar ma sai da aka farfasa cibiyar sadarwa ta musamman ta NCC a Kano, inda aka sace kayaiyaki na biliyoyin Naira.
Da yake zantawa da manema labarai a jiya Juma’a, Musa ya bukaci masu zanga-zangar da su gane cewa barna ba ta da amfani kuma zai jefa al’ummar kasar cikin rudani.
Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya bukaci Tinubu ya saurari koken jama’a
Yayin da yake yabawa rundunar ƴansandan Najeriya bisa kokarin da take yi na tabbatar da zaman lafiya, ya kara da cewa za a tilastawa sojoji shiga lamarin idan har aka ci gaba da samun tashin hankali.
Ya ce: “Ya kamata mu gane cewa wadannan barna da kudaden mu aka samar da su kuma da kudaden mu za a gyara su idan kuka bata.
“Don haka maimakon yin haka, ya kamata mu hada kai don tabbatar da cewa babu wani abu. ya lalace,” in ji shi.