Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano ya yi Allah-wadai da afkuwar munanan al’amura yayin gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar.
Kwamitin ya bayyana hakan ne ta cikin wani saƙon murya da shugaban sakatariyar (Amb. Ibrahim Waiya) ya aikowa kadaura24, ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bashir A Bashir.

Kwamitin zaman lafiyar ya bayyana takaicinsa bisa yadda matasa suka ba da ƙofa ga wasu suka rika amfani da su wajen lalata kadarorin gwamnati, da na ƴan kasuwanni da sunan siyasa.
Amb. Waiya ya cigaba da cewa tun farko shugabannin zanga-zangar suna da laifi duba da yadda aka bayyana musu abun da ka iya faruwa idan suka ce sai sun gabatar da wannan zanga-zanga amma su ka yi burus da wannan kiraye-kiraye su ka fita sai gashi abunda suke hange ya afku.
Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya bukaci Tinubu ya saurari koken jama’a
Waiya ya kuma nuna takaicin sa bisa kwashe kayan ofishin hukumar Sadarwa ta ƙasa dake hanyar zuwa gidan gwamnati, inda ya ce ba iya kanawa ne su ka yi asara ba har da jihohin arewa maso gabas, domin shi ne guri ɗaya tilo da Najeriya ta samar domin koyar da al’ummar arewa harkokin sadarwa.
A ƙarshe Waiya ya ja hankalin masu haɗa wannan husuma, inda ya tunatar dasu gobe ƙiyama domin rai zata girbi duk abinda ta shuka.