Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya bukaci Tinubu ya saurari koken jama’a

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjinawa ‘yan Najeriya da suka fito kan tituna domin nuna adawa da gwamnatin babban abokin hamayyarsa a zaben da ya gabata.

Kadaura24 ta ruwaito cewa Atiku ya fafata da Shugaba Bola Tinubu a zaben bara, inda ya zo na biyu.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Atiku ya yabawa ‘yan Najeriya bisa jajircewar da suka nuna, yayin da ya yi Allah wadai da bata garin da suka shiga cikin yan zanga-zangar domin yin sace-sace a wasu jihohin.

Talla
Talla

Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su lura da yadda suke gudanar da aikinsu da kuma daina muzgunawa ‘yan jarida da harbe-harbe babu gaira babu dalili.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta zamo mai sauraron koken al’umma.

Zanga-zanga:APCn Kano ta mayar da zazzafan martani ga kalaman gwamna Abba Kabir

“Yadda al’umma suka fito a ranar farko domin yin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin kasar abun a yaba musu ne. Wadannan zanga-zangar ta bude wata hanya mai mahimmanci ga jama’a don nuna rashin amincewa da manufofin gwamnati, don ta dauki matakan da suka dace don ciyar da kasar gaba.”

“Yawancin masu zanga-zangar sun gudanar da ita cikin kwanciyar hankali da lumana kuma dole ne a yaba musu saboda kamun kai da juriyar da suka nuna, Sai dai a wasu wuraren an sami rahotannin tashe-tashen hankula, lamarin da ya kai ga jami’an tsaro sun dauki matakai .

“Ina kira ga masu zanga-zangar da su tabbatar da sun gudanar da ita cikin lumana lumana tare da yin kira ga ‘yan Najeriya da su kara nuna goyon bayansu ga zanga-zangar lumana ta adawa da tsadar rayuwa da kawo karshen mulkin zulunci”.

“Ina kuma kira ga ‘yan sanda da su kara kaimi wajen gudanar da aikinsu bisa kwarewa. Su dai yiwa masu zanga-zangar kisan gilla da cin zarafin su ba gaira ba dalili. Dole ne ‘yan sanda su guji cin zarafin ‘yan jarida da ke ba da rahoton zanga-zangar. Ya zama wajibi hukumomin tsaro su yi taka-tsantsan wajen tabbatar da doka da oda.

Waɗanda Suka Yi Zanga-Zanga A 2012 Na Kokarin Danne Haƙƙin Yan Nigeria — Atiku

“Ina karfafa gwiwar hukumomin tsaro da su gano tare da ware wasu tsirarun bata gari da su ke yin ta’addanci da sace-sacen kayan gwamnati da na jama’a, tare da tabbatar da cewa abin da wasu ‘yan tsiraru ke yi ba zai lalata zanga-zangar lumana da mafi yawan yan kasa ke yi ba.

“Ga gwamnati, ina yi muku gargaɗi da ku zamo masu sauraren koken jama’a. Lokaci ya yi da za ku himmatu domin biyan bukatun masu zanga-zangar. Al’ummar kasar na ba za su iya cigaba da kasancewa cikin tsadar rayuwa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...