Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun tarwatsa wasu matasa da su ka yi yunkurin kutsawa cikin wani shago da ke kan titin gidan Zoo a babban birnin jihar.
Wadanda ake zargin sun yi yunkurin kutsawa cikin ginin bene mai hawa biyu na Shagunan Sadaraki dake Kan titin zoo road.
Sai dai ‘yan sandan sun yi gaggawar shiga domin dakile matakin nasu.
Amma kafin isowar jami’an tsaro, waɗanda ake zargin sun lalata tagogin ginin.
Dama gwamnati da Dattawa sun yi hasashen hakan ka iya faruwa a lokacin da aka fito zanga-zangar.
Sai dai rundunar yan sandan Nigeria ta ce ta yi shirin ko ta kwana domin dakilewa da kama wadanda su ka yi yunkurin lalatawa sace dukiyoyin al’umma da sunan zanga-zanga.
Alfijir labarai