Yadda masu zanga-zanga suka fara kone-kone a kofar gidan gwamnatin Kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna adawa da wahalhalun da ake fama da su a fadin Nigeria, sun fara kona tayoyi a kofar gidan gwamnatin jihar Kano a safiyar ranar Alhamis.

Masu zanga-zangar da su ka fito daga sassa daban-daban na birnin Kano sun yi dandazo ne a gidan gwamnati, inda gwamna Abba Kabir Yusuf zai yi musu jawabi.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar ne suka hada tayoyi, kuma suka banka musu wuta a lokacin da suke tunkarar kofar.

Hakan ya sanya jami’an tsaron da ke gidan gwamnati suka harba bindiga sama da barkonan tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Hakan tasa masu zanga-zangar suka rika guduwa zuwa wurare daban-daban .

Sai dai zuwa yanzu abubuwa sun daidaita domin jami’an tsaro su yi nasarar hana kona tayoyin , Inda suka bukaci masu zanga-zangar da su gudanar da zanga-zangar cikin lumana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...