Zanga-zanga: Yadda harkokin Kasuwanci suka tsaya chak a Nigeria

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Harkokin Kasuwanci sun tsaya chak sakamakon fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a manyan birane dake jihohin Nigeria baki daya.

A jihohin Kano, Kaduna Legos Fatakwal da Abuja bankuna da kasuwanci sun kasance a rufe da sanyin safiyar wannan rana ta alhamis saboda zanga-zanga da ake gudanarwa a fadin kasar.

Manya hanyoyi suma sun kasance babu kowa yayin da masu zanga-zangar suka bijirewa kiraye-kirayen da mahukunta suka rika yi na dakatar da zanga-zangar.

Talla
Talla

Titunan da aka saba samun cunkoson jama’a a Kaduna babu kowa, yayin da masu zanga-zangar suka fito kan tituna suna nuna korafe-korafen su game da tsadar rayuwa suke ciki.

Haka a Kano ma Mutane sun fito a manyan titunan jihar sun dauke da kwalaye da ke nuna bukatarsu ta dawo da tallafin man fetur da dawo da darajar naira da kuma magance tsadar kayan abinchi.

Hotunan Yadda Matasa da Dattawa Su ka Fito Zanga-zanga a Kano

An rufe bankuna, kasuwanni, da sauran wuraren kasuwanci a Owerri saboda fitowar masu zanga-zangar kamar yadda gidan talabijin na Channels suka rawaito.

Tsayarwar harkokin Kasuwanci a Manyan biranen Nigeria na nuni da cewa tattalin arzikin Nigeria zai sami nakasu sosai, saboda komai ya tsaya ballantana gwamnati ta sami kudaden shiga.

Waɗannan suka shirya zanga-zangar sun bayyana cewa za su kwashe kimanin Kwanaki 10 suna gudanar da zanga-zangar ta adawa da tsadar rayuwa a Nigeria.

Sai dai rahotannin da jaridar kadaura24 ke samu sun nuna cewa an jibge tarin jami’an tsaro a wurare daban-daban a dukkanin jihohin tarayyar Nigeria, don ganin zanga-zanga ba ta rikide ta koma tashin hankali ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...