Kamfanin sadarwa na MTN ya rufe ofisoshinsa da ke faɗin Najeriya a yau Talata.
Matakin kamfanin ba ya rasa nasaba da yadda wasu abokanan hulɗarsa da aka rufewa layin waya suka yi cincirindo a ofisoshin kamfanin har ma wasu suka yi ƙoƙarin kutsa kai don neman a buɗe masu layukan nasu.

MTN ya rufe layukan mutane saboda sun gaza haɗa lambarsu ta ɗan ƙasa da layinsu.
Da dumi-dumi: Gwamnan kano ya turawa majalisar dokoki sunan wanda zai nada a matsayin kwamishina
MTN ya wallafa sanarwar rufe ofisoshin nasa a shafinsa na X inda ya ce “ku sani cewa ofisoshinmu a faɗin Najeriya za su kasance a rufe yau 30 ga watan Yulin 2024.”