Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sunan wani tsohon soji ga majalisar dokokin jihar kano domin tantace shi a matsayin kwamishina.
Wanda aka tura din shi ne Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya.

Shugaban majalisar Isma’il Falgore ne ya karanta wasikar da gwamnan ya tura musu, Yayin zaman majalisar na wannan rana ta talata.
Majalisar ta bukaci wanda aka tura sunan na sa da ya gurfana gaban majalisar gobe laraba domin tantancewa.