Zanga-zanga: Gwamnatin tarayya ta ba da sanarwa kan gidajen yari

Date:

 

 

A daidai lokacin da ake sa ran za a fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Nijeriya a ranar 1 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta ayyana dukkanin gidajen gyara hali 256 da ke fadin Nijeriya a matsayin β€œwuri Mafi hatsari” inda ta yi gargadin cewa, kada a keta alfarmar su a kowane irin hali.

Talla
Talla

Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Gidajen fursuna na Kasa (NCoS), Halliru Nababa, ne ya yi wannan gargadin a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, ACC Abubakar Danlami Umar, ya sanya wa hannu a madadinsa ranar Talata a Abuja.

Nababa ya bayyana cewa, β€œSaboda zanga-zangar da aka ce za a gudanar a ranar farko ta watan Agustan 2024, hukumar kula da gidan gyara hali ta Nijeriya na son sanar da jama’a cewa, an sanya duk gidajen gyara hali na Nijeriya a matsayin β€˜jar danja’; don haka, duk wani mutum ko gungun mutanen da ba su da hurumi, kar a gansu a wuraren.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related