Da dumi-dumi: Tinubu ya rage farashin Shinkafa a Nigeria

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Gwamnatin Najeriya ta ce ta rage farashin buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 da kashi 50 zuwa N40,000 a fadin kasar.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi ranar Litinin a Abuja.

Talla
Talla

A cewarsa, rage farashin shinkafar ya zo ne a daidai lokacin da aka tura motocin dakon kaya 20 ga gwamnonin jihohi daban-daban domin rabawa ‘yan Najeriya.

Za mu duba tare da bayar da magunguna kyauta ga marasa lafiya a karamar hukumar Wudil – Bilkisu Indabo

Ya ce sun kuma rage farashin Shinkafar da kusan kashi 50 na kudinta ga yan Nigeria, tuni an tura Shinkafar wurare daban-daban a jihohin kasar nan domin sayar da ita akan farashin naira dubu 40. An samar da cibiyoyi, ta yadda masu bukatar wannan shinkafa za su je can su saya a kan Naira 40,000,” inji shi.

A halin da ake ciki kuma, wani binciken da kadaura24 ta gudanar ya nuna cewa ana sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 tsakanin N75,000 zuwa N80,000 a wasu daga cikin Kasuwannin Kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...