Zanga-zangar: Yan Kasuwar Kano sun yi shirin samar da tsaro a wuraren Kasuwancinsu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Kungiyar dattawa yan kishin Najeriya, ta sake neman masu shirya zanga-zanga ta kasa da su zauna domin tattaunawa don samar da maslaha, hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar Kano suka samar da jami’an tsaro na musamman gaggawa domin samar da tsaro a kasuwanni da wuraren kasuwanci a yayin zanga-zangar da za a yi a fadin kasar.

Da suke jawabi yayin wani taron gaggawa da wakilai daga manyan Kasuwannin kano da manyan masu super market, shugaban dattawan masu kishin kasa, Dr Bature AbdulAziz da Alhaji Sabi’u Bako shugaban ‘yan kasuwar Kano, sun bayyana bukatar daukar kwararan matakai na dakile satar dukiyar jama’a.

Sai dai Shugaban Dattawan, Dokta Bature AbdulAziz, ya tunatar da cewa, zanga-zangar ba ta haifar da da mai ido, sai dai tana jefa al’umma cikin bala’i da rashin tabbas.

Talla
Talla

Ya kara da cewa kamata ya yi masu shirya zanga-zangar da zauna tare da gwamnati don gabatar da bukatunsu don warware matsalolin cikin lumana mai makon zanga-zangar.

A yayin taron, shugaban kungiyar hadakar ‘yan kasuwa ta kasa, Alhaji Bature Abdul Aziz ya kaddamar da kwamitin mambobi 20 domin tsara yadda jami’an tsaron sa kan zasu yi aiki.

Sanata Kwankwaso ya fitar da matsayarsa kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Nigeria

A jawabinsa a wajen bikin, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Balarabe Tatari, ya bukaci matasa da su daina yin ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Balarabe Tatari ya ce, rahotannin da ke tafe na nuni da cewa za a gudanar da zanga-zangar cikin lumana, duk da cewa ya zama wajibi mu samar da isassun matakan kare Kano a matsayin cibiyar kasuwanci.

Ya bayyana cewa suna sane da cewa a irin wannan yanayi, munanan abubuwa sukan shiga su mayar da ita wani abu na daban ta hanyar wawashe da lalata dukiyar al’umma ”.

Shugaban ya ce “Ina kira ga matasa da su sanya a ransu cewa Kano ce gidansu kuma duk wani yunkuri na ganin an zaunar da jihar lafiya kar su Kawo masa cikas .

Ya jaddada cewa “Kano jihar mu ce, mu hada kai don ganin ba a karya doka da oda ba”.

Talla

A nasa bangaren, Manajan Daraktan Hukumar Kula da Kasuwar Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Hamisu Saadu Dogon Nama ya yi kira ga dukkanin masu yin Kasuwanci a Kantin Kwari da su bi umarninsu tare da ba da gudummawar kason su don tabbatar da doka da oda.

Hakazalika, Manajan Daraktan Kasuwannin Sabon Gari/ Galadima da Kasuwan Singa, Alhaji Abdullahi ya ce “Mun sanar da ‘yan kungiyarmu da su fito a ranar zanga-zangar domin kare wuraren kasuwancinmu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...