Dizal dinmu na da ingancin da za a yi amfani da shi ko’ina a duniya – Matatar Dangote

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Matatar man Dangote ta sake tabbatar da cewa man dizal din da take fitar wa ya cika duk wasu ka’idoji da ya kamata dizal ya cika a duniya, musamman idan aka kwatanta da wanda ake shigo da shi daga kasashen waje.

Wannan dai na zuwa ne dangane da kalaman da babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed ya yi a baya-bayan nan, cewa man dizal din matatar Ɗangote bai kai wanda suke shigo da shi ƙasar nan inganci ba.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito matatar ta ce babu daya daga cikin dizal din da ake shigowa da shi Najeriya da zai iya yin gogayya da na matatar Dangote ta fuskar inganci kuma duk wani kwararre da ke da niyyar gwada kayayyakinmu da wadanda ake shigo da su kai tsaye za su iya tabbatar da hakan.

Talla
Talla

Babban jami’in kasuwanci na rukunonin kamfanin Dangote, Rabiu A. Umar ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Kano a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.

Ba ma tsaron a gwada Ingancin dizal ɗinmu a ko’ina a duniya, mun fara da 600-700 PPM saboda sabo ne.

“Yanzu, dizal din na mu yana kan 87 PPM, kuma a karshen watan Agusta, zai koma 10 PPM.

Fara aikin matatar mu ya karya farashin man dizal a kasuwa – Matatar Dangote

A cewarsa, ko a lokacin da shugaban majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya ziyarci matatar man a karshen makon da ya gabata, a kan hanyarsu ta zuwa ne suka yanke shawarar sayen man dizal daga gidajen mai guda biyu, idan aka kwatanta da na matatar man Dangote; sun yi mamakin sakamakon ingancin dizal din mu da suka gani.

“Gwajin da aka gudanar a gabansu ya tabbatar da ingancin man dizal din namu kuma ya tabbatar da cewa dizal din namu na daya daga cikin mafi inganci a duniya wanda me da karancin sinadarin sulfur,” inji Umar.

“Gwajin ya nuna cewa man dizal na matatar Dangote yana da sinadarin sulfur na ppm 87.6, yayin da sauran samfuran biyu suka nuna matakan adadin sinadarin sulfur da yake cikin nasu ya wuce 1800 ppm da 2000 ppm.

“Muna samar da dizal mafi kyau a Najeriya. Abin ban takaici ne cewa maimakon a yaba mana, kuma sai ake kushe mana .”

Sanata Kwankwaso ya fitar da matsayarsa kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Nigeria

”Kofofinmu a bude suke ga duk wasu hukumomi ko dai-dai kun al’umma da suke son gudanar da gwaje-gwaje kan samfuranmu kowane lokaci”.

Har ila yau, dangane da batun matatar man mu cewa har yanzu ba ta da lasisi, Rabi’u Umar ya bayyana cewa suna da duk wasu takardu da hujjojin da ba za su yi karya ba, inda ya kara da cewa an bi dukkan hanyoyin da suka dace kafin matatar ta fara aiki.

”Kowa zai iya binciko takardun mu, hukumomi sun ba mu lasisi kafin mu fara aiki”.

“Aiyukan da kamfanin NNPC ya yi a matatar mu yanzu ya kai kashi 7.5 bisa kashi 20”

Da yake magana game da daidaiton kamfanin na NNPC a matatar Dangote, Umar ya ce da farko kashi 20% an baiwa hukumar ta NNPC da wasu ayyuka da ake sa ran karasawa.

Talla

Ya kara da cewa idan aka kammala aiki, ana sa ran za ta iya sarrafa kusan ganga 650,000 na danyen mai a kowace rana, wanda za ta zama matatar mai ta gaba-gaba cikin mafi girma a duniya.

Ya bayyana matatar Dangote a matsayin abin alfaharin Najeriya da Afirka wanda bai kamata a rika yi mata zagon kasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...