Fara aikin matatar mu ya karya farashin man dizal a kasuwa – Matatar Dangote

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

Matatar mai ta Dangote ta ce tun lokacin da man dizal din matatar ya shiga kasuwa daga watan Afrilun 2024 farashin dizal din ya karye daga N1,600 zuwa N1,000 kowace lita.

Ko da yake a halin yanzu dizal ya dan haura naira N1,000.

Matatar tace akalla farashin ya sauka da sama da kashi 30 cikin 100 a kasuwa, saukar farashin zai yi tasiri sosai a dukkan bangarorin tattalin arziki da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki a Nigeria.

Talla
Talla

Babban jami’in kasuwanci na rukunonin Dangote, Rabiu A. Umar ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Kano a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.

Umar ya ce tun da matatar man Ɗangote ta fara aiki, baya ga kasuwannin Najeriya, ana fitar da kayayyakinta zuwa kasashen Afirka da Turai da kuma Amurka.

Sanata Kwankwaso ya fitar da matsayarsa kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Nigeria

“A yanzu da nake magana da ku, muna ta tace Jet-A 1, wato man jiragen sama da dizal tare da sa ran fara fitar da man fetur daga wata mai zuwa,” in ji Umar.

SolaceBase ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne bayan tsokacin da babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA) Farouk Ahmed ya yi a baya-bayan nan na cewa ingancin man da matatar ta ke fitarwa ya yi kasa da man da ake shigowa da su daga kasashen waje.

“Har yanzu a baiwa matatar Dangote lasisin fara cikakken aiki ba, ” in ji Ahmed.

Talla

“Ba mu ba su lasisi ba tukunna.

Da yake mayar da martani kan wannan tsokaci, Babban Jami’in Harkokin Kasuwancin Rukunonin Dangote ya musanta ikirarin, inda ya ce kalaman kokarin yiwa matatar man Ɗangote zagon kasa ne kawai .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...