Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Sufeto Janar na ‘yan sandan Nigeria Kayode Egbetokun, ya bukaci dukkanin kungiyoyin da ke shirin shiga zanga-zangar da za a yi a fadin kasar nan da su mika bayanansu ga kwamishinonin ‘yan sanda a jihohinsu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da cewa an gudanar da zanga-zangar cikin lumana.

Egbetokun ya ce, “Mun amince da ‘yancin da kundin tsarin mulkin Najeriya bai wa yan kasa na yin zanga-zangar lumana.
“Duk da haka, domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da zaman lafiya, muna kira ga dukkan kungiyoyin da ke shirin gudanar da zanga-zangar da su yi wa Kwamishinan ‘yan sanda cikakken bayani akan su a jihar da ake son gudanar da zanga-zangar.
Rundunar yan Sandan Nigeria ta gano masu shirya zanga-zanga irin ta Kenya a ƙasar
“Domin ganin an gudanar da ba cikin nasara muna fatan masu shirin yin zanga-zangar su za su ba da bayanans kamar haka: jihar da za a yi zanga-zangar, hanyoyin da za a gudanar da zanga-zangar; tsawon lokacin da ake san za a yi zanga-zangar, ran gudanar da zanga-zangar; da sunaye da bayanan shugabannin zanga-zangar da masu shirya zanga-zangar.”
IG ya kara da cewa bayanan da ake sa ran daga masu shirya zanga-zangar sun kuma hada da matakan za a dauka don hana satar aikata laifuka yayin zanga-zangar, da dai sauransu.
Ya kara da cewa ta hanyar bayar da bayanan, ‘yan sanda za su iya tura isassun ma’aikata da kayan aiki domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.
Ya kuma ce akwai bukatar ‘yan sanda su san takamaiman hanyoyi da wuraren da za a gudanar da zanga-zangar domin kaucewa rikici da wasu al’amura da ka iya tasowa.

Egbetokun ya ce sauran ka’idojin sun hada da, “samar da hanyoyin sadarwa ta shugabannin zanga-zangar don magance duk wata damuwa ko matsalolin da ka iya tasowa .
“Muna kira ga duk masu zanga-zangar da su ba ‘yan sanda hadin kai, ta hanyar bin doka, don tabbatar da samun nasarar gudanar da ‘yancinsu.”