Gwamnan Kano ya yi alwashin kawo karshen matsalar ruwa a masarautar Rano

Date:

 

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alwashin kawo karshen matsalar ruwa a yankin masarautar Rano.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karbi mai Martaba Sarkin Rano Amb. Muhammad Isa Umaru Wanda ya kawo masa gaisuwar sallah a gidan gwamnati.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce tuni gwamnati ta umarci kwararrun injiniyoyi su bincika Yadda za’a janyo ruwa daga madatsar ruwa ta Tiga zuwa masarautar Rano da kewayanta.

InShot 20250309 102403344
Talla

Kazalika gwamna Abba Kabir Yusuf yace duk da cewa yankin masarautar Rano yanki ne da yake kewaye da manyan duwatsu, ya bada tabbacin gwamnati zata haka rijiyoyin birtsatse na zamani domin kawo karshen matsalar ruwa da yankin ke fuskanta.

Ya ce gwamnatinsa zata bawa yankin masarautar Rano fifiko na musamman wajen samar da hanyoyi da inganta al’amuran kiwon lafiya da harkar noma da samar da ayyukan yi ga matasan yankin.

A A Zaura ya mika ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi

Da yake jawabi tunda farko, mai Martaba Sarkin Rano Amb Muhammad Isa Umaru ya mika koken alumarsa na karancin ruwa da masarautar ke fuskanta tare da godiya ga gwamnan Kano bisa cigaba da aikin titin kilo Mita biyar na karamar hukumar Rano.

Daga nan ya mika ta’aziyyarsa dana al’umar masarautar Rano bisa rasuwar galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi wanda aka yi jana’izarsa a jiya Laraba.

Ya kuma jajantawa al’umar jihar Kano baki daya bisa kisan gillar da aka yiwa yan asalin jihar Kano a jihar Edo inda ya jaddada Kira da ayiwa iyalan wadanda aka kashe adalci ta hanyar biyan diyya da kuma hukunta duk wadanda aka samu da hannun cikin wannan ta’asa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...