Tsohon dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Alhaji Abdulkarim Abdulsalam A A Zaura, mika sakon ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano kuma babban dan majalisar masarautar Kano, Alhaji Abbas Sunusi Bayero, wanda ya rasu yana da shekaru 92 .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Hadimin tsare-tsarensa (Protocol) Baba Yawale ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.
A A Zaura ya bayyana marigayi Galadiman Kano a matsayin wani dattijo mai daraja wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban Kano da kuma sha’anin sarauta a arewacin .

“Rasuwar Alhaji Abbas Sunusi babban rashi ne, ba ga iyalansa kadai ba, har ma ga daukacin Masarautar Kano da kuma al’ummar jihar baki daya, domin mutum ne mai hikima da rikon amana, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma.” Inji A A Zaura
Alhaji Abdulkarim Abdulsalam, ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashin.
Hawan Sallah: Ƴansanda sun sake gayyatar Hadimin Sarki Sanusi kan zargin bijirewa umarni
“Ina mika ta’aziyyata ga Abdullahi Abbas shugaban jam’iyyar APC na Kano da daukacin iyalan Galadima, Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi Aljanatul Firdaus,” Inji Zaura
Idan za a tunawa Kadaura24 ta rawaito Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sunusi rasuwa a daren ranar Talata, inda ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.
An haife shi a shekarar 1933 a garin Bichi na jihar Kano, ya taba zama Wamban Kano kafin Sarki Sanusi Lamido Sanusi ya nada shi sarautar Galadiman Kano a shekarar 2014.
Galadiman Kano ya ba da gudunmawa sosai wajen cigaban harkokin Masarauta da abubuwan da suka shafi shugabanci a Kano.
Tuni dai aka gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar nan suka halarta.